Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata



Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun shiga ofishin shugaban ƙaramar hukumar Gaya a Jihar Kano, Hon. Mahmoud Tajo Sani, inda suka sace wasu kayayyaki, ciki har da kayan da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan yau da kullum na hukumar.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin labarai, Kwamared Naziru Mukhtar Gaya, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce fashin ya faru ne da daren ranar Talata.

Ya bayyana abin da ya faru a matsayin “abin kunya da takaici.”

“An yi sata a ofishin shugaban ƙaramar hukumar Gaya, Hon. Mahmoud Tajo Sani, wasu ɓata-gari sun sace muhimman kayayyaki,” in ji shi.

Ko da yake bai bayyana darajar kayan da aka sace ba, ya ce hukumomin tsaro sun fara bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin.

Ya yi Allah-wadai da wannan lamari, tare da roƙon Allah Ya tona asirin waɗanda suka aikata laifin kuma Ya kare ƙaramar hukumar Gaya daga irin wannan lamarin.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *