Ɗalibar SS3 Ta Sace Kanta, Ta Karɓi Kuɗin Fansa Naira 500,000 Daga Mahaifiyarta
[ad_1]
Rundunar Ƴansandan Jihar Delta ta cafke wata dalibar SS3 mai shekara 17, Chiamaka, bisa zargin shirya satar kanta tare da karɓar kuɗin fansa Naira 500,000 daga mahaifiyarta. Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya bayyana hakan a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cewarsa, ɗalibar ta haɗa baki da wasu ƙawayenta uku wajen aiwatar da shirin. Ta bar Ugolo zuwa Fatakwal inda suka sauka a wani otal, sannan ta kira mahaifiyarta tana iƙirarin cewa an sace ta tare da neman kuɗin fansa.
- Gwamnati Za Ta Tura Runduna Ta Musamman Jihar Kwara Da Neja
- Kisan Woro A Jihar Kwara Ya Bayyana Rugujewar Tsaron Karkara A Nijeriya — Gbenga Hashim
Rahotanni sun ce mahaifiyar, wadda bazawara ce kuma manomiya, ta sha wahala wajen tara kuɗin, tana neman taimako daga mutane daban-daban kafin ta sanar da ƴansanda. Binciken jami’ai ya gano cewa ba satar gaskiya ba ce, inda ake zargin ɗalibar ta amsa laifin a hannun ƴansanda.
A cikin bidiyon da rundunar ta fitar, ta ce ita da ƙawayenta ne suka shirya satar kanta domin karɓar kuɗi daga mahaifiyarta, tana mai cewa an rinjaye ta ne bayan ta fara ƙin amincewa. Ta ce kuɗin da aka karɓa an kashe su ne wajen sayen kaya.
Edafe ya gargaɗi cewa irin wannan ɗabi’a ta fara yawaita a tsakanin matasa masu shekaru 15 zuwa 20, yana mai cewa ɗaya daga cikin ƙawayen da ake zargi ta taɓa aikata makamancin haka a baya, lamarin da ya ƙarfafa musu gwuiwa su ma su gwada sa’arsu.
[ad_2]
Source link