Zulum ya ƙara wa CJTF da ’yan banga albashi da kashi 80 cikin ɗari

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Borno ta yi ƙarin kaahi 80 cikin 100 a alawus na wata-wata ga ’yan sa-kai na Civilian JTF da ’yan banga da mafarauta da masu sa-ido na unguwanni.

Gwamna  Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa sabon ƙarin zai fara aiki daga watan Janairu 2026, da nufin ƙara wa ’yan sa-kai ƙwarin gwiwa, ya inganta ayyukansu, tare da ƙarfafa su wajen ci gaba da tallafawa rundunonin tsaro.

A sanarwar da mashawarcin gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya fitar, ya ce gwamnan ya yi ƙarin alawus ɗin kowanne ɗan sa-kai daga naira 30,000 zuwa Naira 50,000, yayin da shugabannin ƙungiyoyin za su riƙa karɓar Naira 150,000.

Dauda ya ce dukkan waɗanda abin ya shafa ’yan sa-kai ne a ƙarƙashin shirin Borno Youth Empowerment Scheme.

Wannan mataki na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen tallafa wa waɗanda ke sa rayuwarsu a haɗari domin kare al’umma da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Borno.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa ƙungiyoyin CJTF, ’yan banga da mafarauta sun kasance ginshiƙai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram, suna cike gibi tare da rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019, gwamnan ya fara daga alawus daga naira 15,000 zuwa 20,000, sannan daga baya zuwa 30,000.

Zulum ya kuma yaba da gudummawar da suka bayar, ciki har da kama manyan shugabannin ’yan ta’adda da kuma bayar da bayanan sirri da suka taimaka wajen hana hare-hare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamnan ya yi kira ga ’yan sa-kai da su ci gaba da jajircewa, su riƙe ɗa’a, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *