Zaɓen 2027: A raba wa ’yan Najeriya shinkafa — Tinubu
[ad_1]
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci ƙungiyar da ke mara masa baya domin sake tsayawa takara a zaɓen 2027 mai suna, ‘Renewed Hope Ambassadors’ da ta raba wa ’yan Najeriya shinkafa a wannan lokaci da Musulmi ke azumin watan Ramadana da kuma azumin mabiya addinin Kirista na Lenten.
RFI ya ambato Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma wanda ke jagorancin ƙungiyar yana bayyana hakan tare da sanar da cewar ’ya’yan ƙungiyar za su aiwatar da shirin a kowane sashe na ƙasar.
Uzodinma ya ce umarnin ya nuna irin tausayin da shugaban ƙasa ke da shi da kuma karamci ga ’yan ƙasa tare da neman haɗin kan jama’a, a daidai lokacin da su ke sadaukar da rayukan su wajen ibada da taimako da kuma kula da juna.
Sai dai wasu na kallon wannan yunƙuri a matsayin wani shirin kamfe na zaɓe mai zuwa gabanin kaɗa gangar siyasa, la’akari da cewar wannan rabon ana yin sa a tsakanin magoya bayan jam’iyya.
Raba shinkafa ga talakawa ya zama ruwan dare a ƙarƙashin gwamnatin APC tun da ta karɓi mulkin Najeriya a shekarar 2015.
Yanzu haka ’yan siyasa daga jam’iyyu daban daban na can su na raba wa jama’a shinkafar domin rage musu raɗadin halin ƙunci da suka samu kansu da zummar samun goyan bayan su lokacin zaɓuɓɓuka.
A baya gwamnatin Tinubu ta sha sanar da shirye-shiryen tallafa wa jama’a domin rage tasirin tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da ke addabar ƙasar, ciki har da rabon hatsi daga rumbun ajiyar gwamnati da kuma wasu shirye-shiryen tallafin jin ƙai.
Sai dai masu sukar gwamnati na cewa irin waɗannan rabon kayan abinci na ɗan lokaci ne kawai, kuma ba su magance matsalolin tattalin arziki da talauci da yawancin ’yan Najeriya ke fuskanta ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link