Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa

[ad_1]



Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa.

Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano.

An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa.

Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure.

Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis ɗinsa da ke sakateriyar Ƙaramar Hukumar Rano.

Da yake yi wa ma’aikata da magoya bayansa jawabi, Yau, ya gode wa Allah da Ya tsare masa mutuncinsa.

Sannan ya gode wa Majalisar Dokokin jihar da ta wanke shi.

Ya yi godiya ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Gwamna Abba Kabir Yusuf, shugabannin NNPP da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen dawo da shi kan kujerarsa.

Tun farko an dakatar da shi ne bayan kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe na majalisar ya miƙa rahoton wucin-gadi.

Rahoton ya zarge shi da aikata ba daidai ba, cin zarafin ofishinsa, karkatar da dukiyar jama’a da kuma aikata rashin gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen gwamnati.

Sauran zarge-zargen sun haɗa da haifar da rikici tsakanin shugabannin siyasa, sayar da taki sama da farashin da gwamnati ta ƙayyade, da kuma rashin bayyana gaskiya wajen karɓar kuɗaɗen haraji na kasuwanni.

Haka kuma an zarge shi da sayar da rumfunan kasuwa ba bisa ƙa’ida ba.

Yanzu da an wanke shi daga dukkanin zarge-zargen, ya koma bakin aikinsa a matsayin Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *