Za mu gudanar da babban taronmu duk da gargaɗin INEC — ADC

[ad_1]



Jam’iyyar ADC ta ce za ta ci gaba da shirinta na gudanar da babban taronta, duk da gargaɗin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya gargaɗi jam’iyyar da kada ta gudanar da da babban taronta, inda ya ce hakan na iya saɓa umarnin kotu.

Amma ADC ta yi watsi da wannan gargaɗi, tana mai cewa INEC ba ta fahimci hukuncin kotun daidai ba.

“ADC ta ga ya dace ta yi bayani domin gyara wasu kurakurai na fahimtar doka da gaskiya. Duk da cewa hukumar na cewa tana aiki bisa doka da adalci, maganganun shugaban nata sun nuna kuskuren fahimtar ƙa’idojin kundin tsarin mulki da umarnin kotu,” in ji jam’iyyar.

Jam’iyyar ta zargi INEC da wuce gona da iri wajen aikinta, tana ƙoƙarin dakatar da ayyukanta.

Ta bayyana cewa umarnin kotu ya buƙaci a ci gaba da tafiyar da abubuwa yadda suke, ba wai a dakatar da harkokin cikin gida na jam’iyya ba.

“ADC za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa doka, kuma tana kira ga INEC da ta tsaya a kan aikinta na kundin tsarin mulki. Babu wata kotu da ta hana mu gudanar da taronmu,” in ji jam’iyyar.

Har ila yau, ADC ta ce rikice-rikicen cikin gida ba za su hana ta gudanar da ayyukanta na dimokuraɗiyya ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *