Za a kafa kamfanin ƙera kayan sola a Kano
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za a fara ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki daga hasken ranar a jihar.
Hakan a cewar gwamnatin ya biyo bayan samun masu zuba jari a fannin na makamashi, bayan rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanoni biyu da suka shahara a fannin, wato Tricell Solar Solutions da IRS Green Energy..
An kulla yarjejeniyar ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA) domin bayar da shawarwari na fasaha da daidaita ayyuka, a yayin taron Sabunta Makamashi na Najeria (NERIF) na 2025 da aka gudanar a ranar Talata a birnin Abuja, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana.
Ya ce shugaban hukumar Zuba Jari ta jihar (Kan-Invest), Naziru Halliru ne ya jagoranci ƙulla yarjejeniyar a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sansusi ya ce ƙulla yarjejeniyar na cikin manyan matakai da gwamnatin ke ɗauka domin faɗaɗa samar da makamashi mai tsafta da araha, bunƙasa masana’antu a cikin gida, da samar da ayyukan yi ga al’ummar jihar.
Sanarwar ta kuma ce a karkashin wannan tsarin, kamfanin IRS Green Energy zai gina masana’antar kera kayan amfani da hasken rana da ke da ƙarfin samar da 600MW a shekara, yayin da Tricell Solar Solutions zai kafa wata da ke da ƙarfin 500MW, lamarin da ya ce zai mayar da Kano cibiyar samar da sabon makamashi a yankin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link