Zaɓen 2027: ADC Ta Yi Alƙawarin Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro A Arewa Maso Yamma
[ad_1]
Daga Shehu Yahaya
Jam’iyyar adawa ta ADC a shiyyar Arewa maso Yamma ta kara jadadda kudirinta na magance matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin, idan har ta samu damar rike madafun iko a zabukan shekarar 2027 masu zuwa.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ADC na kasa mai wakiltar shiyyar Arewa maso Yamma, Malam Jafaru Sani, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da wakilinmu a Kaduna, jim kadan bayan kammala wani babban taron jam’iyyar da aka gudanar a jihar.
- Hukumar Kula Da Alkalai Ta Haramta Wa Lauyoyi 34 Zama Masu Shari’a A Nijeriya
- Dalilin Ɗage Sauya Sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf Zuwa 12 Ga Janairu
Malam Jafaru Sani ya ce jam’iyyar ADC tana da tsare-tsare masu inganci da za su taimaka wajen shawo kan matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma da ma kasa baki daya, tare da kawo gyara a bangaren harkokin shari’a domin tabbatar da adalci da zaman lafiya.
Ya kara da cewa lokaci ya yi da al’ummar Nijeriya za su rungumi sabuwar tafiya da hadakar jam’iyyar ADC, domin ceto kasar nan daga mawuyacin halin da take ciki, wanda ya alakanta da gazawar jam’iyyar APC mai mulki.
A cewarsa, ADC jam’iyya ce da ke da hangen nesa, manufofi na gaskiya, da jajircewar shugabanni da za su iya kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar ‘yan Nijeriya, musamman a fannonin tsaro, tattalin arziki da adalci.
Jam’iyyar ADC ta yi kira ga al’ummar Arewa maso Yamma da su hada kai da jam’iyyar domin gina kasa mai inganci, tsaro da ci gaba mai dorewa a nan gaba.
Shugaban yace jam’iyyar APC mai mulki ta gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, tare da kasa cika alkawuran da ta dauka ga al’umma tun bayan hawanta mulki.
Malam Jafaru Sani ya jaddada cewa ADC jam’iyya ce da ke da nagartattun shugabanni, manufofi masu ma’ana da kuma tsari mai karfi da zai iya kawo sahihin sauyi a Najeriya, musamman a fannoni irin su tsaro, tattalin arziki, ilimi da shari’a..
Hakazalika, yayi kira ga al’ummar Arewa Maso Yamma da su mara mata baya domin samar da tsaro, adalci da ci gaba mai dorewa a Nijeriya.
[ad_2]
Source link