’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutum 14 da ake zargi da ta’amali da miyagun ƙwayoyi da kuma aikata wasu laifuka daban.

Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar.

A cewar SP Shiisu, jami’an rundunar sun kama mutanen ne a wurare daban-daban da suka haɗa da Dutse, Guri, Babura, Kanya Babba, Bulangu da kuma ‘Yankwashe.

Ya ce rundunar ta ƙwato miyagun ƙwayoyi iri-iri da suka haɗa da Exol guda 8,271, D5, Tramadol, Diazepam, Sholisho, Sukudayin, tabar wiwi, da kuma kuɗi Naira 235,225.

SP Shiisu, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da farautar duk wanda yake da hannu a harkar.

Ya ƙara da cewa za su gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu da zarar sun kammala bincike, domin su fuskanci hukuncin da ya dace da laifukansu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *