Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja
[ad_1]
Wata gobara ta tashi a ranar Laraba ta ƙone kasuwar katako da ke kusa da Jabi Masallaci a Abuja.
Gobarar ta lalata kaya da kayan gini na miliyoyin kuɗi, amma ba a yi asarar rai ba.
Kawo yanzu dak ba a san musababbin tashin gobarar ba.
Sai dai wasu rahotanni na cewa gobarar na iya farawa ne sakamakon matsalar wutar lantarki, wanda wani lokacin wayoyin wuta na faɗowa kan rumfunan kasuwa.
’Yan kasuwa da mazauna yankin sun yi ƙoƙarin kashe wutar, amma ta yaɗo cikin sauri saboda katako da sauran kayayyakin gini na da saurin kamawa da wuta.
Wasu gine-gine da ke kusa da kasuwar sun lalace, lamarin da ya tilasta wa jama’a gudu domin tsira da rayukansu.
Daga baya jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya sun isa wajen tare da kashe wutar.
Mutanen da abin ya shafa sun roƙi gwamnati ta taimaka musu, domin sun rasa duk abin da suka dogaro da shi wajen kula da rayuwarsu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link