’Yan Najeriya sun biya ’yan bindiga N2.57bn a matsayin kudin fansa a shekara ɗaya – Rahoto
[ad_1]
Wani rahoto da cibiyar SBM Intelligence ta fitar ya nuna cewa ’yan bindiga sun karɓi aƙalla Naira biliyan 2.57 a matsayin kudin fansa daga wurin waɗanda suka yi garkuwa da su tsakanin Yuli 2024 zuwa Yuni 2025 a Najeriya.
Rahoton, wanda aka saki a ranar 19 ga watan Disamba, 2025, ya yi nazari kan manyan abubuwan tattalin arziki da siyasa da ke tasiri a Afirka a shekarar 2025.
Ya gano cewa ’yan bindiga sun nemi aƙalla Naira biliyan 48 a matsayin kudin fansa a cikin wannan shekara guda, duk da cewa an biya ɗan ƙaramin kaso ne daga cikin wannan adadi.
SBM Intelligence ta ce alkaluman sun nuna cewa garkuwa da mutane a Najeriya ta rikide zuwa kasuwanci mai riba, wanda ke kara habaka a cikin yanayin raunin gwamnati, faɗin kasa da kuma tabarbarewar tsaro a sassa da dama na ƙasar.
A cewar rahoton, aƙalla mutane 4,722 aka yi garkuwa da su a cikin hare-hare 997 a tsawon lokacin, yayin da aka kashe mutane 762 a hare-haren da suka shafi ’yan bindiga da tashin hankali.
Kodayake bukatar kudin fansa ta ƙaru sosai a naira, SBM Intelligence ta lura cewa a darajar dala, abin da ’yan bindiga suka samu bai karu ba saboda faduwar darajar naira.
Naira biliyan 2.57 da aka biya a fansa a wannan lokacin ya yi daidai da kusan dala miliyan 1.66, wanda ya ɗan fi dala miliyan 1.13 daidai da Naira miliyan 653.7 da aka karɓa a shekarar 2022.
Arewa maso Yamma ta ci gaba da zama cibiyar garkuwa da mutane
Arewa maso Yamma ta ci gaba da mamaye fagen garkuwa da mutane a Najeriya, inda ta samu hare-hare 425, ko kuma kashi 42.6 cikin 100 na dukkan hare-haren da aka yi a ƙasar.
Yankin ya kuma samu mutane 2,938 da aka yi garkuwa da su, wanda ya kai kaso 62.2 cikin 100 na dukkan wadanda aka sace.
Jihar Zamfara ce ta fi yawan wadanda aka yi garkuwa da su da mutum 1,203, sai Kaduna da Katsina.
SBM Intelligence ta danganta yawan garkuwa da mutane a yankin da faɗin yankunan karkara da kuma kasancewar manyan ƙungiyoyin ’yan bindiga da ke gudanar da manyan hare-hare ba tare da wani ƙalubale ba.
A gefe guda, yankin Kudu maso Yamma ya fi ƙarancin hare-haren garkuwa da mutane, inda ya samu kashi 5.3 cikin ɗari na hare-haren da aka yi da kuma kashi 3 cikin ɗari na wadanda aka sace.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link