‘’Yan Najeriya ba su mance da badaƙalar da aka tafka a gwamnatin Jonathan ba’
[ad_1]
Fadar Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa duk da tana maraba da tsayawa takarar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Zaɓen 2027, amma ya kwana da sanin cewa har yanzu ’yan ƙasar ba su mance da badaƙalar da aka tafka a lokacin gwamnatinsa ba.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar da yammacin ranar Litinin, ta ce ’yan Najeriya na sane da “rashin takaɓus” a mulkin Jonathan ɗin na shekarun baya.
Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar mai taken “Muna maraba da tsohon shugaban ƙasa zuwa takarar shugabancin ƙasa”, “amma ’yan Najeriya na sane da munanan ayyukansa lokacin yana mulki.”
Fadar shugaban ƙasar ta kuma bayyana yunƙurin jam’iyyar PDP na tsayar da Jonathan takara, a matsayin “raguwar dabara” sakamakon rawar da ya taka wajen ruguza tattalin arziki Najeriya, a tsawon shekaru 16 da PDPn ta kwashe tana mulkin ƙasar.
Sanarwa ta ce matuƙar Jonathan ya yanke shawarar tsayawa takarar, zai fuskanci matsalolin kundin tsarin mulki da bai ba shi damar sake tsayawa takara ba, la’akari da cewa an taɓa rantsar da shi har sau biyu a matsayin shugaban ƙasa, a gefe guda kuma ga ƙalubalen jama’a.
Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga kalaman da tsohon ministan yaɗa labarai kuma jigo a jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana, ya yi wanda ya nuna cewa Jonathan zai iya komawa kan mulki a ƙarƙashin inuwar PDP.
A baya-bayan nan ne Jerry Gana, ya bayyana cewa tshohon shugaban ƙasar wanda ya sha kaye a hannun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a 2015, shi ne ɗan takara ɗaya tilo da ka iya kayar da Tinubu a zaɓen da ke tafe na 2027.
Sai dai fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da batun na Farfesa Gana, inda ta bayyana shi a matsayin mafarki irin na siyasa, har ma ta gaargaɗi Jonathan da ya ankare da makamantan waɗannan kalamai da ke fitowa daga bakin ’yan PDP ɗin da suka watsar da shi tsawon shekaru 12, kar su kai shi su baro.
Goodluck Jonathan ya mulki Najeriya a daidai lokacin da ƙungiyar Boko Haram ke kan ganiyarta wajen ƙaddamar hare-hare kan fararen hula.
A baya-bayan nan dai akwai ƙaruwar kiraye-kiraye tsakanin wasu ’yan jam’iyyar hamayya ta PDP kan tsohon shugaban ƙasar ya fito takara a Zaɓen 2027.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link