Yadda Ɗalibai Ke Ɗaukar Darasi A Ƙasa, Cikin Rana Da Ƙarƙashin Bishiyoyi A Bauchi
[ad_1]
Duk da aikin gyaran makarantu da ake ci gaba da yi a faɗin Jihar Bauchi, ɗaliban Makarantar Firamare ta Unguwar Harɗo da ke yankin Miri, ƙaramar hukumar Bauchi, har yanzu na karɓar darasi a ƙarƙashin zafin rana da inuwar bishiyoyi saboda rashin ajujuwa masu kujeru.
Wakilinmu ya gano cewa ɗaliban na fuskantar matsaloli wajen samun yanayi mai kyau na karatu, duk da ƙoƙarin malamai na ci gaba da koyarwa. ‘Yan jarida sun lura da wannan mummunan yanayi ne a ranar Alhamis yayin rangadin duba makarantu da Hukumar SUBEB ta jihar Bauchi ta yi a yankin Bauchi ta Kudu domin bibiyar fara zangon karatu na shekarar 2026/2027.
- Gwamnan Bauchi 2027: Kungiya Ta Fara Nema Wa Farfesa Pate Kuri’a
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Bisa Zargin Luwaɗi Da Ƙananan Yara A Bauchi
Tawagar da Mallam Abbas Abdulmumini, Daraktan sashin Kula da Bibiya da Tantancewa na SUBEB, ya jagoranta, ya nuna rashin jin daɗi game da rashin ganin shugabar makarantar a bakin aiki. Ya jaddada cewa gwamnatin jihar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Shugaban SUBEB, Alhaji Adamu Muhammad Duguri, ba za ta amince da sakaci da aikin gwamnati ba.
Sai dai Mallam Abdulmumini ya yaba wa al’ummar yankin bisa gina sabon ginin ajujuwa, tare da nuna gamsuwa da yawan ɗaliban da ke makarantar.
A wani ɓangarem kuma, Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Mohammed Lawal Rimin Zayam, ya bayyana cewa matakin gyaran makarantu na nuna ƙudurin Gwamna Bala Mohammed na samar da yanayin karatu mai kyau, inda ya ce mataki na farko ya shafi makarantu 252, yayin da wasu 256 suka riga suka samu tantancewa domin shiga kashi na biyu na aikin.

[ad_2]
Source link