Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni
[ad_1]
A safiyar Litinin ɗin nan ƙungiyar Hamas ta saki rukunin farko na ’yan ƙasar Isra’ila bakwai da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza.
A ɗaya ɓangaren kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako.
Tuni jami’an kungiyar agaji ta Red Cross suka shiga gidan yarin Wada a safiyar domin ɗaukar wani fursuna Bafalasdine da za fitar, wanda ke fama da rashin lafiya.
Hamas ta mika su ne ga kungiyar Red Cross a Gaza a yayin da ake da ran sako wasu ƙarin mutum 13 na gaba a Litinin ɗin nanm a cewar hukumomin Isra’ila.
Wannan na faruwa ne a yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya taka muhimmiyar rawa a sulhun, yake ziyara a ƙasar Isra’ilan a safiyar Litinin.
Wannan na zuwa ne bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da ɓangarorin biyu suka sanya hannu a kai a baya-bayan nan.
A bangare guda kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako, a matsayin ɓangarenta na musayar fursunonin yaƙin.
Ma’aikatar Harkokin Gida ta Isara’ila ta fitar da jerin sunayen mutanen da aka saki da shekarunsu:
- Esiitan Ibrahim Mor,
- Gali Berman, 28
- ZIV Berman, 28
- Omri Maran, 48
- Alon Ohel, 24
- Guy Gilboa-Dalal, 24
- Matan angrest, 22
Na gaba ake da ran muka su ga iyalansu a wani sansanin soji a Kudancin Isra’ila.
A ɗaya bangaren kuma kungiyar kula da Fursunoni ta Palastinu ta fitar da jerin sunayen mutane 1,718 da Isra’ila za ta sako.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link