WHO ta buƙaci Amurka ta fitar da bayanai kan asalin COVID-19

[ad_1]



Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta buƙaci Amurka ta bayyana duk wasu bayanan sirri da take da su game da asalin cutar COVID-19, duk da cewa Amurkan ta fice daga cikin hukumar.

Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce wasu ƙasashe musamman Amurka sun taɓa cewa suna da bayanan sirri kan asalin cutar, amma har yanzu ba su miƙa wa WHO waɗannan bayanai ba, duk da wasiƙun da aka aike musu watanni da suka gabata.

Cutar Coronavirus ta kashe kusan mutum miliyan 20 a faɗin duniya, tun bayan ɓullarta a garin Wuhan na ƙasar China a ƙarshen 2019.

WHO ta ce gano asalin cutar na da matuƙar muhimmanci domin hana sake aukuwar irin wannan annoba a gaba.

A watan Janairun 2025, Shugaban Amurka Donald Trump wanda yake goyon bayan zargin cewa cutar ta ɓarke ne daga wani ɗakin gwaje-gwaje a Wuhan, ya sanar da ficewar ƙasarsa daga WHO, yana zargin hukumar da sakaci wajen tafiyar da lamurran da suka shafi annobar.

Sai dai WHO ta ce har yanzu bincikenta bai kammala ba, kuma dukkan ƙofofinta na binciken na nan a buɗe.

Kazalika, ta kuma roƙi duk wata gwamnati da ke da bayanai kan asalin cutar ta gaggauta bayyana su.

A halin yanzu, Amurka na bin WHO bashin kusan dala miliyan 260 na kuɗaɗen mambobinta na shekarun 2024 da 2025.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *