Wata Ƙungiya Ta Mara Wa Ganduje Baya Don Zama Daraktan Kamfen Ɗin Tinubu A 2027
[ad_1]
Ƙungiyar National Agenda For Tinubu 2027 (NAFT.27) ta bayyana goyon bayanta ga Abdullahi Umar Ganduje. Ta ce shi ne mafi dacewa ya zama Darakta Janar na kamfen ɗin sake zaɓen Bola Tinubu a 2027.
A wata sanarwa da jagoranta, Dr. Aliyu Ibrahim, ya fitar a Abuja ranar Alhamis, ya fayyace hujjojinsa. Ya jaddada cewa gogewar Ganduje a matsayin tsohon shugaban APC na ƙasa ta ƙara tabbatar da cancantarsa.
- Ganduje Ya Musanta Zargin Nasir El-Rufai Kan Ɓacewar Dadiyata
- HOTUNA: Ɗan Ganduje Ya Ziyarci Kwankwaso A Kano
Ya kuma bayyana cewa Ganduje ya taka rawa wajen daidaita jam’iyyar da aiwatar da sauye-sauye masu muhimmanci. Haka kuma ya ambaci gudunmawarsa wajen kafa cibiyar horaswa ta APC a Abuja.
Ibrahim ya ƙara da cewa Ganduje na da ƙwarewar jawo gwamnoni daga jam’iyyun adawa zuwa APC. Ya ce wannan ƙwarewa za ta taimaka wajen tafiyar da kamfen cikin tsari da nasara.
Ƙungiyar ta buƙaci Shugaba Tinubu ya yi la’akari da naɗin Ganduje domin jagorantar kamfen ɗinsa. Ta ce yana da tasiri a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.
Wannan goyon baya na zuwa ne yayin da APC ke ƙara shirye-shiryen zaɓen 2027. Ana kallon matakin a matsayin wani ɓangare na dabarun ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓe.
[ad_2]
Source link