Uba Sani ya yi wa ma’aikatan manyan makarantu ƙarin kashi 70 a albashi
[ad_1]
Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da aiwatar da ƙarin kashi 70 a albashin ma’aikatan dukkanin makarantun gaba da sakandare na gwamnati da ke jihar.
Sabon tsarin albashin na CONPCASS/CONTEDISS 2024 wanda zai fara aiki daga Oktoban 2025, na daga cikin kokarin gwamnatinsa na inganta walwalar ma’aikata da farfaɗo da harkar ilimi a jihar.
Amincewar na zuwa ne bayan wani muhimmin zama da aka gudanar tsakanin gwamnan da shugabannin ƙungiyoyin ma’aikatan manyan makarantu (JUTIKS), wanda hakan ya kai ga janye yajin aikin da aka shafe wata guda ana yi.
Taron wanda Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta shirya kuma aka gudanar a fadar gwamnatin Kaduna, ya samu halartar shugabannin ƙungiyoyi daga Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zariya, da Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya, da kuma Kwalejin Nazarin Jinya da Ungozoma ta Kaduna.
Ana iya tuna cewa, tun a ranar 30 ga watan Satumban da ya gabata ne ma’aikatan manyan makarantun suka tsunduma yajin aikin neman a aiwatar da tsarin albashi na CONPCASS/CONTEDISS na 2009, da kuma inganta fansho da walwalar ma’aikata gaba ɗaya.
A wani taron manema labarai da shugabannin ƙungiyoyin suka gudanar, sun yaba da jajircewar gwamna Uba Sani wajen kare haƙƙin ma’aikata da bai wa ilimi fifiko.
Haka kuma, sun jinjina wa gwamnatin bisa rage kuɗin makaranta da kashi 50% a dukkanin manyan makarantu, da kuma gyare-gyaren gine-gine da kayan aiki da ake ci gaba da yi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link