Tsohon ɗan takarar Gwamnan PDP a Yobe ya koma ADC
[ad_1]
Tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Yobe, Dokta Ali Garba Tikau, ya koma jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Wakilinmu ya ruwaito cewa Tikau ya yi takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP a 2011 da 2023.
Dokta Tikau, wanda tsohon Babban Sakatare ne a Hukumar Ilimi ta Firamare ta Ƙasa , ya sanar da sauya sheƙarsa a mazaɓarsa ta Tikau a ƙaramar hukumar Nangere.
A jawabinsa ga magoya baya da membobin ADC, Tikau ya bayyana jajircewarsa ga jam’iyyar kuma ya ce ta ɗauki wannan mataki tare da mutanensa.
“Bayan mun yi wa PDP hidima cikin kwanciyar hankali tsawon shekaru da dama, daga bisani mun yanke shawarar shiga ADC don ci gaban al’ummarmu baki ɗaya,” in ji shi.
“Mun ƙuduri aniyar yin iya baƙin ƙoƙarinmu don tabbatar da nasarar ADC a zaɓen 2027 a dukkan matakai.”
Tikau ya miƙa katinsa na PDP a hukumance ga Samaila Jalamawa, shugaban jam’iyyar na yankin Tikau.
Da yake tarbar ɗan siyasar da ya sauya sheƙa, Shugaban jam’iyyar ADC a yankin Tikau, Babangida Dagare, ya yi masa maraba da zuwa.
Dagare ya tabbatar da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da jajircewa don cimma nasara a babban zaɓen 2027.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link