Tinubu ya naɗa sabon Sufeto Janar na ’Yan sanda
[ad_1]
Rahotanni na cewa Shugaba Bola Tinubu, ya naɗa Tunji Disu a matsayin sabon Sufeto Janar na ’Yan Sanda (IGP), inda ya maye gurbin Kayode Egbetokun.
Gidan talabijin na Arise TV ya ruwaito wata majiya na tabbatar da naɗin a wannan Talatar.
Majiyar, wadda ta ba da tabbacin sanarwa a hukumance za ta fito nan ba da jimawa ba, ta ce naɗin sabon Sufeto Janar ɗin na zuwa ne bayan dakatar da Kayode Egbetokun daga muƙaminsa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link