Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya

[ad_1]



Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙar sanar da shi sabon naɗin da ya yi.

Naɗin Janar Musa na zuwa ne kwana guda bayan murabus ɗin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin saboda dalilai na rashin lafiya.

Musa wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 har zuwa Oktoban 2025 lokacin da Shugaban Kasa ya sauke shi daga muƙamin a watan Oktoba, bayan wani yunkurin juyin mulki da aka yi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *