Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga El-Rufai kan rasuwar mahaifiyarsa
[ad_1]
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyya zuwa ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, bisa rashin mahaifiyarsa, Hajiya Umma, wadda ta rasu a ƙasar Masar bayan ta yi fama da rashin lafiya.
A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanugaya ya fitar, ya bayyana marigayiyar mahaifiyar El-Rufai a matsayin uwa wadda rayuwarta abin koyi ne, sannan ta tarbiyyartar da ’ya’ya da jikoki waɗanda suka ba da gagarumar gudunmawa ga ƙasarmu.
Wani bangare na sanarwar ya ce: “Nasir, don Allah ka amshi saƙon ta’aziyya ta na ban-kwanan ga mahaifiyarka, Hajiya Umma, wadda rasuwarta ta afku a yau a birnin Alkahira. A matsayina na wanda ni ma na taɓa rashin uwa, ina taya ka alhinin wannan rashi. Na san yadda raɗaɗin wannan rashi yake.”
“Rasa uwa wani irin raɗaɗi ne wanda babu kamarsa. Na sani cewa babu wasu kalmomi da za su iya magance baƙin cikinka gaba ɗaya, amma ina roƙon Allah da ya gafarta mata.
Ina kuma fatan ka samu haƙurin juriya daga kyakkyawar rayuwar da ta yi da kuma ɗabi’un da ta dasa a cikin iyalan baki ɗaya.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link