Tinubu ya buƙaci sojoji su ci gaba da martaba dimokuraɗiyya

[ad_1]



Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci rundunar sojin Najeriya da su kasance masu ladabi, haɗin kai da kuma martaba dimokuraɗiyya.

Ya bayyana sojoji a matsayin ginshiƙin wajen haɗin kan ƙasa da kuma kare dimokuradiyyar Najeriya.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa sojoji domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar nan.

Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, a lokacin bikin Tunawa da ’Yan Mazan Jiya na shekarar 2026 tare da bikin karrama wasu jami’ai.

Ya ce a matsayinsa na Babban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya, yana kira ga dakarun da su kasance masu biyayya, ladabi, aminci da haɗin kai.

Ya ƙara da cewa a ƙasa mai al’ummomi da yawa kamar Najeriya, sojoji su ne ginshiƙin ƙarfin haɗin kanta.

Shugaban ya buƙaci sojoji da su kasance masu biyayya ga Kundin Tsarin Mulki da dimokuraɗiyya, tare da buƙatar kare iyakokin ƙasar.

Tinubu ya ce walwalar sojoji tana da alaƙa kai-tsaye da tsaron ƙasa.

Ya tabbatar da cewa za a inganta kayan aiki, horo da yanayin rayuwar sojoji.

Yayin da yake karrama ’yan mazan jiya da suka rasa rayukansu wajen kare ƙasa, Shugaban ya ce ba za a taɓa mantawa da su ba, domin za su kasance cikin zukatan ’yan Najeriya.

Ya yaba wa dakarun da ke kan gaba wajen fuskantar barazana, inda ya bayyana cewa nasarorin da suka samu a baya-bayan nan sun taimaka wajen samar da tsaro da kwanciyar hankali a yankuna da dama.

Haka kuma ya yaba wa iyalan sojoji, inda ya ce su ma sun taka muhimmiyar rawa wajen tsaron ƙasar.

Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa duk da ci gaban da aka samu a ‘Renewed Hope’, gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai kowane ɗan ƙasa ya samu damar yin rayuwa da aiki cikin tsaro da mutunci.

Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), da tsohon kakakin rundunar Doji, Birgediya Janar Sani Usman (mai ritaya), da saurannsu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *