Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
[ad_1]
’Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Mata, Super Falcons, sun yi barazanar ƙaurace wa wasannin sada zumunta da Najeriya za ta buga a watan Disamba mai kamawa.
’Yan wasan sun ce za su ƙaurace wa wasannin ne idan har Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ci gaba da jinkirta biyan kuɗaɗen alawus-alawus da suke biyo tun na Gasar Olympics da aka yi a birnin Paris a 2024.
Wasu majiyoyi daga ƙungiyar sun tabbatar cewa ’yan wasan na ci gaba da jiran a biya su haƙƙoƙinsu na wasannin da suka buga, ciki har da alawus na nasarar da suka samu a gasar Olympics, duk da cewa Najeriya ta fice tun a matakin rukuni bayan shan kashi a hannun Brazil da Spain da Japan.
Wani jami’in tawagar, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce ’yan wasan gaba ɗaya sun amince cewa ba za su halarci kowanne wasa ba muddin ba a biya su haƙƙoƙinsu ba.
Ana sa ran Najeriya za ta buga jerin wasannin sada zumunta daga ranar 2 zuwa 10 ga watan Disamba, a wani ɓangare na shirye-shiryen Super Falcons domin tunkarar gasar cin Kofin Afrika ta Mata na 2026.
A halin yanzu, NFF ba ta fitar da jerin sunayen ’yan wasan da za su wakilci Najeriya a wasannin ba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link