Sojoji Sun Kama Ɗan Ƙunar Baƙin Wake A Borno

[ad_1]

Sojojin Operation Hadin Kai sun kama wani da ake zargin ɗan ƙunar baƙin wake tare da ƙwace kayayyakin haɗa bama-bamai a Jihar Borno.

An gudanar da aikin ne bayan samun sahihin bayanan sirri domin tabbatar da tsaron garin Banki da ke Karamar Hukumar Bama.

  • Sin Ta Gabatar Da Shirin Inganta Lafiyar Yara Da Matasa Na Nan Zuwa Shekarar 2030
  • Jami’ar MDD: Kasar Sin Babbar Ginshiki Ce Ta Cinikayyar Duniya

An kama wanda ake zargin a ranar Litinin a Masallacin Banki Central.

An same shi da kayan fashewa da aka riga aka shirya tayar da su, lamarin da ke nuna cewa yana shirin kai hari.

A halin yanzu ana yi masa tambayoyi domin gano masu ɗaukar nauyinsa da alaƙarsa da ƙungiyoyin ta’addanci.

A wani ɓangare na aikin, sojoji sun tare wata mota ƙirar Peugeot ɗauke da buhun takin urea a kan iyakar Nijeriya da Kamaru.

Ana amfani da wannan taki wajen haɗa bama-bamai.

Bincike ya ƙara kai ga kama wani dillalin takin tare da gano wasu ƙarin buhuna, wanda ya kai adadin da aka ƙwace zuwa buhu 12.

Duk waɗanda aka kama da kayan da aka ƙwace suna hannun sojoji domin ci gaba da bincike.

Rundunar sojin ta ce tana ci gaba da sintiri da ayyukan tsaro domin hana hare-hare da kare fararen hula a faɗin yankin Arewa maso Gabas.










[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *