Sin Ta Fitar Da Mizanin Kasa Na Kyautata Nagartar Na’urar Adana Lantarki

[ad_1]

A yau Juma’a ne kasar Sin ta fitar da wani mizani na kasa baki daya, wanda zai tabbatar da nagartar karfin na’urar adana lantarki, da nufin kyautata daukacin matakan kare na’urorin.

Tun daga ranar daya ga watan Afirilun shekarar 2027, sabon mizanin zai fara aiki bisa jerin matakai masu tsauri na cimma nasarar da aka sanya gaba. Burin shi ne kyautata tsaron runbunan adana lantarki yayin yanayin na matsi, kamar lokacin fuskantar tsananin zafi, da lokacin da na’urori suka yi caji fiye da kima, da kuma idan sun fuskanci kalubalen takura a wuri guda.

Ma’aikatar raya masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ce ta tsara mizanin, wanda ake fatan zai zurfafa ikon kiyaye kasuwar fannin, da ingiza daga matsayin fasahohinsa, da kyautata kare abokan hulda daga hadurra da kuma tabbatar da hakkokinsu. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *