Shugabancin Ƙungiyar Kasuwar Singa (SIMDA) Ya Karyata Rahoton Tashin Sabuwar Gobara A Kasuwar
[ad_1]
Shugabancin Ƙungiyar Kasuwar Singa (SIMDA), ƙarƙashin jagorancin Barrista Junaidu Muhammad Zakari, ya karyata rahoton da ke yawo na cewa an sake samun wata sabuwar gobara a kasuwar.
A cewar Sakataren Shugaban Ƙungiyar kuma Mai Taimaka Masa a Kafafen Yaɗa Labarai, Ambasada Abubakar Usman Ali, hayakin da wasu suka gani a kasuwar ya samo asali ne daga gobarar da ta faru a baya, wadda ake ci gaba da ayyukan shawo kanta.
- GORON JUMA’A
- APC Ta Maye Gurbin Uzodimma Da Masari A Matsayin Shugaban Kwamitin Babban Taronta Na Ƙasa
Ya ce jami’an Hukumar Kashe Gobara, tare da sauran hukumomin da abin ya shafa, suna nan a harabar kasuwar domin tabbatar da tsaro da kuma hana duk wani abu da ka iya haddasa matsala.
Shugabancin SIMDA ya yi kira ga ’yan kasuwa da al’umma baki ɗaya da su kwantar da hankalinsu, tare da gujewa yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tantance ba, yana mai cewa hakan na iya haifar da firgici da ruɗani.
Ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sahihin bayani ta hanyoyin da suka dace, yayin da ake ci gaba da ɗaukar matakan tabbatar da tsaro a kasuwar.
[ad_2]
Source link