Harin Amurka ya jefa mu cikin fargaba – Mazauna kauyen Sakkawato
[ad_1]
Mazauna garin Jabo a ƙaramar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto sun shiga tsananin fargaba da daren Alhamis bayan Amurka ta kaddamar da hare-haren bama-bamai a kan ’yan ta’adda a garin.
Lamarin ya faru ne kimanin ƙarfe 9:30 na dare, inda aka ce ƙarar ta girgiza gine-gine kafin bama-baman su faɗi ƙasa su kama da wuta nan take.
Wani ganau mai suna Attahiru Madawaki Jabo ya bayyana wa wakilinmu yadda abin ya faru da firgici.
“Ina gida lokacin da muka ji ƙarar da ta fito daga wani wuri, wanda ya girgiza gidajenmu sosai. Abin yana faduwa ƙasa, sai ya kama da wuta a wajen garin Jabo,” in ji Jabo.
A cewar majiyoyin yankin, sojojin da ke sansanin bincike a kusa da wurin sun garzaya wurin nan take, suka kewaye yankin, suka tattara sassan na’urar da ta tarwatse sannan suka kai su sansaninsu domin ci gaba da bincike.
Ko da yake ba a samu rahoton asarar rayuka ba, wasu mazauna Jabo a lokacin da ake rubuta wannan rahoto sun ƙi komawa gidajensu saboda tsoron wata fashewa ta sake faruwa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa kasarsa ce ta kaddamar da harin kan wadanda ya kira da ’yan ta’adda, kamar yadda ya wallafa a cikin wani saƙo a shafinsa na Truth Social a daren Alhamis.
A cewar Trump, an kashe ‘yan ta’adda da dama a harin, wanda ya danganta da Ma’aikatar Yaƙin Amurka.
Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kallon suna da matsala ta musamman saboda zargin kisan kare dangi kan Kiristoci.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link