Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Batun Daina Amsar Tsabar Kuɗaɗe Da FAAN Ta Fara
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya amince da dakatar da tsarin daina amsar tsabar kuɗi da Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) ta ƙaddamar a manyan filayen jiragen sama a faɗin ƙasar nan.
A ranar 1 ga Maris, 2026, FAAN ta hana karɓar tsabar kuɗi a ƙofofin biyan kuɗin shiga, inda ta wajabta wa masu ababen hawa amfani da katin cire kuɗi ko kuma turawa ta hanyar banki.
- Darussa Daga Ramadan Na 12: Ƙarfafa Alaƙa Da Alƙur’ani A Ramalana
- Yanzu-yanzu: Burin Nijeriya Na Zuwa Gasar Kofin Duniya Ya Hadu Da Cikas
Sai dai, lamarin ya haifar da tsaiko matuƙa, inda fasinjoji da masu ababen hawa suka maƙale na tsawon sa’o’i sakamakon ruɗani da cunkoson ababen hawa da ya biyo bayan fara aiwatar da tsarin.
Hakan ya haifar da ɓacin rai a tsakanin matafiya, inda wasu suka rasa jiragen da za su hau sakamakon jinkiri, wasu kuma suka samu jinkirin ɗaukar su daga filin jirgin saman.
Da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a ranar Laraba, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce Shugaban ƙasa ya amince da dakatar da tsarin.
Ya ce Shugaban ƙasar ya damu matuka da wahalhalun da ‘yan Nijeriya suka fuskanta, don haka, ya umarci ma’aikatar da ta sake nazari tare da tsara sabon tsari mai inganci kan manufar.