Rangadi zuwa ƙauye ya sa Malamin addini yin takarar Gwamnan Sakkwato

[ad_1]



Sanannen malamin addinin Musulunci a Sakkwato Malam Bashir Ahmad Sani da aka fi sani da Malam Bahar Ɗanfili ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Sakkwato a kakar zaɓe mai zuwa ta 2027.

Malamin ya sanar da ƙudirin nasa a wurin Tafsirin bana a birnin jiha ya ce yanke hukuncin ne biyo bayan rangadin da ya yi ne a ƙauyukka 65 a faɗin jihar Sakkwato domin ya samu ƙorafi da yawa na mutanen jiha.

A cewarsa mutane na buƙatar ɗaukin gaggawa kan matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa da tsadar rayuwa da ke addabar wasu magidanta a jiha.

“Shekara 22 muna yin wa’azi kan karantarwar addinin musulunci, ba mu taɓa zagin kowa ko kuma a ganmu cikin yekuwar zaɓen wata  jam’iya ba,” a cewarsa.

Ya ce, kun yi ta kira da mu yi takara muna cewa, ba mu da sha’awar shiga siyasa kullum kuna yin kiran ina cewa a’a tau yanzu na karɓa.

Malamin bai ambaci jam’iyar da zai tsaya takara ba, a baya kafin nasarar wannan gwamnati ta Ahmad Aliyu suna da kyakkyawar alaƙa da mutanen, bayyana ƙudirin nasa na nuna ba tafiya tare tsakaninsa da gwamnati mai ci ta APC.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *