Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki

[ad_1]



Majalisar Dinkin Duniya ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkumai na karayar tattalin arziki bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar ƙarshe kan shirin nukiliyarta da manyan ƙasashen yammacin Turai.

Birtaniya, Faransa da Jamus ne suka bijiro da batun maido da waɗannan takunkuman a taron kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda aka yi kan saɓa yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015 da Iran ta yi.

Haka kuma, ƙasashen uku sun gargaɗi Tehran kan ɗaukar matakan da za su ƙara dagula lamarin.

“Sake ƙaƙaba takunkuman Majalisar Dinkin Duniya ba yana nufin ƙarshen diflomasiyya ba ne,” in ji ministocin harkokin wajen ƙasashen uku na Turai, da aka fi sani da E3, a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa a ranar Lahadi.

“Muna kira ga Iran da ta guji ɗaukar matakan da za su ƙara dagula lamarin, sannan ta koma bin ƙa’idojin da suka zama dole a ƙarƙashin yarjejeniyoyin tsaron da suka shafi doka,” kamar yadda suka ƙara da cewa.

An dai maido da ɗimbim takunkuman karayar tattalin arziki kan Iran a karon farko cikin shekaru 10 kamar yadda RFI ya ruwaito.

Takunkuman, waɗanda ke zuwa watanni biyu bayan fito na fito tsakanin Iran da Isra’ila, lamarin da ya sa Amurka ta kai wani gagarumin harin bam a tashoshin nukiliyarta, zai haifar da koma-baya ga tattalin arzƙin Iran, wanda ke fuskantar ƙalubale.

Iran ta yi tir da maido da takunkuman, tana mai bayyana matakin a matsayin abin da bai dace ba, inda ta yi kira ga ƙasashen duniya da kada su aiwatar da su.

Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Iran wadda ta bayyana hakan, ta ce babu adalci a wannan matakin, wanda ta ce ya saɓa ƙa’ida.

A halin da ake ciki, tuni Iran ta janye jakadunta a ƙsashen Birtaniya, Faransa da Jamus.

Manyan ƙasashen duniya dai na zargin Iran ne da ƙoƙarin ƙera makaman nukiliya, duba da yadda take ci gaba da tacewa, tare da inganta ma’adinan uranium, zargin da Iran ta sha musantawa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *