Netanyahu ya ba da haƙuri kan harin Isra’ila a Qatar
[ad_1]
Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ba wa Gwamnatin ƙasar Qatar haƙuri kan harin da ƙasarsa ta kai a birnin Doha, wanda ya yi ajalin wani jami’in tsaron Qatar.
Netanyahu ya bayar da haƙuri ne a yayin wata tattaunawa da shugaban Amurka, Donald Trump ya shirya tsakaninsu da Fira Ministan Qatar, Mohammed Al-Thani.
A saƙon da Netanyahu ya wallafa a X, ya ce, “Mai girma Fira Minista, ina sanar da kai cewa Isara’ila ta yi nadamar abin da ya faru na rasuwar wani ɗan ƙasarka a harin da muka kai,” da makami mai linzamina ranar 9 ga watan Satumba a birnin Doha.
Fadar White House ta Amurka da Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar Qatar sun tabbatar da tattaunawar, wadda Shugaba Donald Trump ya jagoranta.
Sanarwar da Fadar White House ta fitar ta ce, Netanyahu, “Ya bayyana matuƙar nadama bisa yadda harin makami mai linzamin ya yi ajalin jami’an tsaron Qatar a bisa kuskure.
“Kazalika ya bayyana nadamarsa da cewa harin da Isra’ila ta kai kan jagororin ƙungiyar Hamas, ya keta hurumin ’yancin Qatar a matsayin ƙasa, yana mai jaddada cewa hakan ba zai sake faruwa ba.”
Idan ba a manta ba a baya Isra’ila ta kai harin ne a yayin ake tattaunawa tsakaninta da wakilan ƙungiyar Hamas a birnin Doha. Ta bayyana cewa ta kai harin ne a kan wasu jagororin ƙungiyar Hamas, tana mai nanata cewa za ta maimaita irinsa idan bukatar hakan ta taso.
Bayan harin ‘—wanda ƙasashen duniya, har da Najeriya suka la’anta—ne Qatar ta dakatar da tattaunawar ɓangarorin Hamas da Isra’ila, wanda ke da nufin ganin ƙungiyar ta sako Isra’ilawan da ta yi garkuwa da kuma tsagaita wuta a Zirin Gaza.
Kazalika ta yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci mummunar ɗabi’ar ta Isra’ila da ke barazana ga tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya ba.
Qatar ta kasance babban mai shiga tsakani domin sasanta rikicin Gaza, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, kuma ita ce mai masauki ga babban sansanin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ta bayyana godiya kan abin da Trump ya yi “Don hana maimatuwar hari kan ƙawarta, ƙasar Qatar, da kuma haɗin gwiwarsu ta fuskar tsaro.”
A saƙon da Netanyahu ya wallafa a X, ya bayyana ce, “Mai girma Fira Minista, ina sanar da kai cewa Isara’ila ta yi nadamar abin da ya faru na rasuwar wani ɗan ƙasarka a harin da muka kai.
“Amma ina so ka fahimci cewa ƙungiyar Hamas ce hadafinmu ba ’yan ƙasar Qatar ba.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link