NDLEA ta kama mutum 143 da miyagun kwayoyi kilo 982.8 a Sakkwato

[ad_1]



Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wani dattijo mai shekaru 72 kan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Jihar Sakkwato.

Kwamandan NLDEA a jihar, Mustapha Muhammad Giɗaɗo, ya ce mutumin yana cikin mutane 146 da hukumar ta kama tare da kwace ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 982.8 a jihar.

Giɗaɗo ya ce ƙwayoyin sun haɗa da kwalaye 54 na maganin tari mai sinadarin codeine da aka kama a iyakar Najeriya da Nijar, da kuma buhuna 15 na tabar wiwi da aka ɓoye cikin garin katako da aka shigo da su daga jihar Edo.

Sauran sun haɗa da buhunan tabar wiwi guda 198 da ƙwayoyin Diazepam da sauran miyagun ƙwayoyi.

Ya ce daga cikin waɗanda aka kama, an riga an yanke wa mutane 13 hukunci, yayin da wasu 18 ke jiran shari’a a kotu.

Ya bayyana cewa an yi wannan nasara ne a watanni hudu da suka gabata, da ya kama aiki a matsayin kwamandan NLDEA a jihar.

Giɗaɗo ya ce ƙara da cewa hukumar ta yi wa masu dogaro da miyagun ƙwayoyi 18 jinya tare da mayar da su cikin iyalansu.

Kwamandan ya danganta nasarorin da suka samu da goyon bayan gwamnatin jihar Sakkwato, haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, da kuma bayanan sirri da jama’a ke bayarwa a kan lokaci.

Ya sake jaddada ƙudirin hukumar na kawar da shan miyagun ƙwayoyi da fataucin su a jihar, yana mai cewa hadin kan jama’a shi ne ginshikin nasarar wannan yaki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *