Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP

[ad_1]



Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ƙaryata jita-jitar ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa YPP.

Rahotanni na yawo a shafukan sada zumunta cewa ya sauya sheƙa, amma mai magana da yawunsa, Gyang Bere, ya ce labarin ƙarya ne, tare da buƙatar jama’a su yi watsi da shi.

Bere, ya ce labarin ƙarya ne aka shirya domin haifar da rikici.

“Wannan zancen ƙarya ne da wasu ke yaɗawa domin su rikita al’umma,” in ji shi.

Ya bayyana cewa gwamnan yana nan daram a jam’iyyar PDP, kuma yana mayar da hankali kan ci gaban al’ummar jihar.

A baya-bayan nan, APC ta yi iƙirarin cewa gwamnan na ƙoƙarin sauya sheƙa zuwa cikinta, amma Mutfwang, ya ce ba shi da niyyar sauya sheka, duk da matsin lambar da yake fuskanta daga wasu.

Sai dai majiyoyi daga PDP sun ce gwamnan na iya komawa wata jam’iyyar a nan gaba, idan rikicin jam’iyyar ya ƙi ƙarewa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *