Muna fama da ƙarancin jami’ai mata a Kano — NDLEA

[ad_1]



Kwamandan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) a Jihar Kano, CN D.Y. Lawal ya nuna damuwa kan ƙarancin jami’ai mata a rundunar a jihar, lamarin da ya bayyana a matsayin babban ƙalubale da ke kawo masu cikas kan ayyukansu.

Lawal ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar don murna da Ranar Mata ta Duniya a Kano a ranar Talata.

Taron wanda CDC Kano, wani shiri na musamman da aka shirya ƙarƙashin Cibiyar Isa Wali Empowerment Initiative, don inganta rayuwar mata.

Shugaban ya ce ƙarancin mata a hukumar na kawo cikas wajen tafiyar da wasu ayyuka yadda ya kamata, musamman waɗanda suka shafi mata.

“Muna da ƙarancin jami’an mata sosai, kuma hakan na shafar ayyukanmu, musamman wajen kula da shari’o’in da suka shafi mata,” a cewarsa.

Kwamandan ya kuma nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar mata masu shiga harkar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar, inda ya ce hakan na buƙatar daukar matakin gaggawa.

Kazalika, ya ƙara da cewa abin damuwa ne yadda mata da yawa ke ƙara shiga harkokin shaye-shaye a wannan lokacin.

A cewarsa, shigar mata cikin hukumar zai ƙara inganta ayyukanta da kuma ƙarfafa ikon ta wajen magance batutuwan da suka shafi jinsi.

Taron ya haɗa mata da matasa daga ƙungiyoyi daban-daban, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi haƙƙin mata, adalci da daidaito.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *