Ministan Tsaro ya faɗi a rumfar zaɓensa

[ad_1]



Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya sha kaye a rumfar zaɓensa yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Garki-Babura a Jihar Jigawa ranar Asabar.

Ministan ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar Ɓaɓura Ƙofar Arewa Primary School 001, inda sakamakon da aka bayyana, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 112, yayin da PDP ta samu 308 a rumfar zabensa.

Zaɓen cike gurbin na Babura-Garki ya fara ne da tsauraran matakan tsaro a fadin mazabar. Jami’an tsaro suka kasance a rumfunan zaɓe da wuraren da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya.

A daidai ƙarfe 8:30 na safe, jami’an Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) sun isa rumfar Garki-Kofar Fada (003) inda suka fara shirye-shiryen zaɓe. Mr Ibrahim Shehu, jami’in zaɓe a rumfar, ya shaida wa manema labarai cewa zaɓen ya gudana lafiya ba tare da wata matsala ta tsaro ko fasaha ba.

A rumfar Primary Yamma (005), Ministar Ƙasa ta Ilimi, Hajiya Suwaiba Ahmad, ta yaba da yadda zaɓen ke gudana cikin kwanciyar hankali. Ta kuma bukaci al’umma su fito su kada ƙuri’a domin jam’iyyar APC. Hajiya Suwaiba ta bayyana kwarin gwiwa cewa APC za ta yi nasara a ƙarshe.

Sai dai, a wasu sassan mazabar, an ga mazauna suna ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, inda aka ga kasuwanci na gudana. Zaɓen ya samu fitowar jama’a mai yawa a yawancin rumfunan zaɓe.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *