Mataimakin Gwamnan Kano Na Iya Yin Murabus Saboda Barazanar Tsige Shi

[ad_1]

Wasu majiyoyi sun bayyana cewar mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, na iya yin murabus biyo bayan barazanar tsige shi.

Majiyoyin sun ce yana duba yiwuwar yin murabus daga muƙamin ne domin kauce wa tsige shi da kuma kare makomarsa ta siyasa.

  • Trump Ya Ce Amurka Za Ta Ci Gaba Da Yaƙi Da Iran Ba Tare da Taimakon Kowa Ba
  • Sarkin Musulmi Ya Ba Da Umarnin Fara Duban Jinjirin Watan Shawwal Ranar Laraba

Rahotanni sun ce dangantakarsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi tsami bayan gwamnan ya koma jam’iyyar APC, yayin da Gwarzo ya ci gaba da zamansa a NNPP.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta soke ma’aikatar da Gwarzo ke jagoranta.

Majalisar Dokokin Jihar ta riga ta ba shi takardar sanarwar tsige shi bisa zarge-zarge da suka haɗa da amfani da muƙaminsa ba daidai ba, karkatar da kuɗaɗe, da sauransu.

’Yan majalisar sun ce ana zargin sa da sama da faɗi da kuɗaɗe masu tarin yawa.

An bai wa Gwarzo kwanaki 14 ya kare kansa.

Idan aka same shi da laifi, za a tsige shi daga muƙaminsa.

Ba a samu jin ta bakinsa ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *