Mataimakin Gwamnan Kano Bai Halarci Sauya Sheƙar Abba Zuwa APC Ba
[ad_1]
Mataimakin gwamnan Jihar Kano, Comrade Abdulsalam Gwarzo, bai halarci taron sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jami’yyar APC ba, abin da ke nuna yiwuwar rashin jituwa a tsakaninsu.
Gwamna Abba, ya ce koma APC ne domin yin aiki tare da gwamnatin tarayya da kuma kawo kwanciyar hankali, ci gaba, da bunƙasa a Kano.
- Da Gaske Ne Wasu Jami’ai 16 Sun Yi Yunƙurin Kifar Da Gwamnatin Tinubu — DHQ
- Mataimakin Gwamna Yusuf Bai Halarci Taron Sauya Sheƙar Maigidansa Zuwa APC Ba
Ya jaddada cewa wannan mataki ba na ƙashin kansa ba ne, kuma ya tabbatar da cewa biyayya da kishin Jihar Kano sun fi komai muhimmanci a wajensa.
Gwamnan ya bayyana cewa shawarar komawa jam’iyyar ta biyo bayan tattaunawa da majalisar gwamnatinsa, shugabannin ƙananan hukumomi, ‘yan majalisa, da sauran masu ruwa da tsaki a siyasa.
Ya ce komawa jam’iyyar da ke mulki a matakin tarayya zai samar da ayyukan ci gaba da inganta yi wa al’umma hidima.
Haka kuma, Gwamnan ya sanar da shirin kafa Kwamitin Manyan Mutane a Kano, wanda zai zama majalisar shawara kan ci gaba da warware rikice-rikice, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta kasance mai haɗa kan kowa da kowa.
Ya kuma yi kira ga al’umma su yi rajista da jam’iyyar APC domin tunkarar zaɓen 2027.
Taron ya samu halartar manyan jami’an APC ciki har da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da sauran shugabanni. Shugaban APC na Kano, ciki har da Abdullahi Abbas.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa sun ce wannan mataki na iya sauya tsarin siyasa a Kano kafin zaɓen 2027.
Da yawa suna ganin rashin halartar mataimakin gwamnan na nuna irin rashin jituwar da ke tsakaninsu wanda hakan zai iya shafar harkokin siyasa a jihar.
[ad_2]
Source link