Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma

[ad_1]



Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya.

Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030.

Golan zai riƙa amfani da riga mai lamba 99 domin ranar haihuwarsa ta 1999, kamar yadda ƙungiyar ta sanar.

A jawabin da ya yi dangane da komawa ƙungiyar, Donnarumma ya ce yana cike da farin ciki da jin daɗi.

“Na koma ƙungiya da ke cike da zaratan ’yan wasa, sannan kuma ƙungiya ce da ke samun horo daga ɗaya daga cikin zaratan masu horar da ’yan wasan ƙwallon ƙafa da aka yi a tarihin tamaula a duniya wato Pep Guardiola.

“Na daɗe ina sha’awar Manchester City. Don haka komawa ƙungiyar abin alfahari ne a gare ni. Buga ƙwallo a filin wasan Etihad zai zama abin alfahari ne a waje na.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *