Mambobin hukumar NAHCON sun buƙaci Tinubu ya cire shugabancin hukumar
[ad_1]
Mambobin kwamitin gudanarwa na Hukumar Aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) sun rubuta takarda ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, suna neman ya cire Farfesa Abdullahi Saleh Usman daga shugabancin hukumar.
Kwamishinonin sun zargi shugaban da cin hanci, rashin iya aiki da kuma yin amfani da mukami ta hanyar da ba ta dace ba.
Ƙoƙarin samun martanin shugaban bai yi nasara ba, domin mai taimaka masa kan kafafen yaɗa labarai, Ahmad Muazu, ya ce yana cikin taro kuma ba za a iya samun sa ba a lokacin.
Sai dai a wata hira da aka yi da shi a baya da jaridar Daily Trust, shugaban ya ce mafi yawan korafe-korafen daga cikin hukumar suna fitowa ne daga ƙiyayya.
“Saboda wani yana jin haushi cewa wasu sun tafi Saudiyya ba tare da shi ba, ko kuma saboda wani ya yi korafi cewa wani ya samu wani abu amma shi bai samu ba,” in ji shi.
Takardar da aka rubuta a ranar 19 ga watan Janairun 2026, na ɗauke da taken “Kuri’ar Rashin Amincewa da Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman.”
Daga cikin Kwamishinonin hukumar da suka sanya wa takardar hannu akwai Farfesa Abubakar A. Yagawal, Yarima Anofi Elegushi, Yarima Aliu Abdulrazaq, Farfesa Muhammad Umaru Ndagi, Alhaji Abba Jato Kala, Sheikh Muhammad Bin Uthman, Dr Tajudeen Abefe Oladejo, Hajiya Aishat Obi Ahmed, Hajiya Zainab Musa, Farfesa Musa Inuwa Fodio da kuma Farfesa Mahfouz A. Adedimeji.
Mambobin kwamitin sun ce neman cire shugaban ya biyo bayan dogon lura da suka yi, sannan duk ƙoƙarin gyara ya ci tura tare da ci gaba da gazawar shugabanci da ta lalata yarda da ingancin ayyukan hukumar.
Sun zargi shugaban da rashin da’a a harkokin kuɗi, suna nuna rashin gaskiya da ayyukan da suka saɓa wa ƙa’idojin gudanar da kuɗin jama’a da hukumar ta kafa.
Haka kuma sun ce ya yi ta kashe kuɗi ba tare da amincewar kwamitin ba, tare da bayar da kwangila fiye da iyakar kasafin da aka amince da shi.
Sun bayyana cewa bayan cikakkiyar tantancewa, “Mun yanke hukunci gaba ɗaya cewa shugaban bai kamata ya ci gaba da zama a ofis ko da kwana ɗaya ba.
“Barinsa a ofis yana jefa shirye-shirye, daidaitawa da gudanar da aikin Hajji mai zuwa cikin haɗari, tare da ƙara jefa Najeriya cikin haɗarin gudanarwa da na diflomasiyya,” in ji mambobin hukumar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link