Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13
[ad_1]
Majalisar Dokokin Jihar Gombe, ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomin ci gaban Ƙananan Hukumomi 13 da Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar.
Ƙudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu cikin rana guda.
Kakakin majalisar, Abubakar Muhammad Luggerewo, ya bayyana hakan ne yayin zaman sauraron ra’ayin jama’a a kan ƙudirin, wanda aka gabatar wa majalisar kwanaki uku da suka gabata.
Ya ce majalisar ta yi gaggawar karanta ƙudirin saboda muhimmancinsa, domin zai taimaka wajen kusantar da gwamnati ga jama’a.
Hakazalika ya ce zai kawo ci gaba a ƙauyuka, da kuma tabbatar da amfani da dukiyar jihar ta hanyar da ta dace.
Kakakin ya ƙara da cewa an shirya sauraron ra’ayin jama’a domin samun shawarwari daga al’umma, shugabanni da ƙungiyoyi domin ƙara wa ƙudirin armashi.
Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a jihar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link