Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba
[ad_1]
Majalisar Dattawa za ta gudanar da zaman tantance manyan hafsoshin tsaron ƙasar a gobe Laraba waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwanan nan.
Shugaba Tinubu ya aike da sunayen sabbin hafsoshin zuwa majalisar ne domin tantancewa da amincewa da su, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.
A wata wasiƙar fadar shugaban ƙasa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman da aka gudanar a wannan Talatar, ya ce kwamitin da ke kula da harkokin tsaro zai zauna gobe domin tantance waɗanda aka naɗa.
A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya aiwatar da sauye-sauye a bangaren tsaro, inda ya ɗaga likafar Laftanar Janar Oluyede Olufemi daga babban hafsan sojin ƙasa zuwa babban hafsan tsaron ƙasa, don maye gurbin Janar Christopher Musa da aka cire daga muƙaminsa.
Haka kuma, shugaban ƙasar ya naɗa sababbin hafsoshin sojin sama, ruwa da ƙasa, yayin da ya bar Manjo Janar E.A.P. Undiendeye a matsayinsa na babban hafsan sashen tattara bayanan sirri na sojin ƙasa.
Sabbin hafsoshin tsaron sun hada da Manjo Janar W Sha’aibu — Hafsan sojojin ƙasa da Air Vice Marshall S.K Aneke — Hafsan sojin sama da kuma Rear Admiral I. Abbas — Hafsan sojin ruwa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link