Ma’aikatan jinya sun fara yajin aiki a Zamfara
[ad_1]
Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi.
Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya.
Ya ce duk da cewa gwamnati ta amince da tsarin CONHESS na ma’aikatan lafiya, amma har yanzu ta kasa aiwatar da tsarin CONMESS na likitoci.
A baya, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, amma ta dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi musu.
Yanzu kuma ƙungiyar ta ce za su ci gaba da yajin aikin daga ranar Asabar har zuwa Talata mai zuwa.
Shugaban ƙungiyar ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ba ta biya musu buƙatunsu ba, ma’aikatan jinyar za su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link