Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Buƙatar Dakatar Da Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano
[ad_1]
Wata Babbar Kotun Tarayya, ta ki amincewa da bukatar bayar da umarnin wucin gadi da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya shigar domin dakatar da shirin tsige shi da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara.
Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a S. M. Shaibu a ranar 25 ga Maris, 2026, ta yanke hukuncin cewa mai karar bai cika ka’idojin da ake bukata domin a bayar da irin wannan umarni na wucin gadi ba.
A wani ci gaba mai alaka da wannan, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta riga ta samu wani umarni na wucin gadi a ranar 11 ga Maris, 2026, wanda ya hana Mataimakin Gwamnan daukar duk wani mataki da zai kawo cikas ga majalisar wajen aiwatar da aikinta na kundin tsarin mulki karkashin sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 (wanda aka gyara).
Cikakken bayani na zuwa daga baya…
[ad_2]
Source link