Iraƙi ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku kan kisan Khamenei
[ad_1]
Gwamnatin Iraƙi ta ayyana zaman makokin kwanaki uku na ƙasa baki ɗaya, sakamakon kisan Jagoran Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Mai magana da yawun gwamnatin Iraƙi, Bassem Al-Awadi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Hukumar Dillancin Labarai ta Iraƙi (INA) ta rawaito a safiyar Lahadin nan.
“Cike da matuƙar baƙin ciki da alhini, muna miƙa ta’aziyyarmu ga al’ummar Iran da kuma dukkan al’ummar Musulmi baki ɗaya kan shahadar malami kuma mujahidi, Jagoran Addini, Mai Girma Ayatollah Sayyid Ali al-Husseini al-Khamenei, wanda muke ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin iyalan Annabi.”
Al-Awadi ya ƙara da cewa kisan ya faru ne “sakamakon wani gagarumin hari na ta’addanci da abin Allah-wadai, wanda ya saɓa wa dukkan ƙa’idojin ɗan-Adam da ɗabi’a, wanda ke karya dokoki da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa a bayyane.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link