HOTUNA: Kwankwasiyya ta ƙaddamar da waƙar ‘Falle Ɗaya’ don adawa da gwamnatin Kano

[ad_1]



Ƙungiyar Kwankwasiyya ta ƙaddamar da sabuwar waƙar “Falle Ɗaya,” wadda mawaƙin ƙungiyar Tijjani Gandu, ya rera, don nuna adawa gwamnatin jihar.

Waƙar ta zo da sabon salo wajen sukar Gwamnatin Jihar Kano.

Mawaƙ Tijjani Gandu ne, ya shirya kuma ya rera waƙar.

An ƙaddamar da ita ne a taron shekara-shekara na bikin kalankuwa da aka yi a gidan jagoran ƙungiyar, Rabiu Musa Kwankwaso, a Kano.

Mutane da dama sun halarci taron, sanye da jajayen huluna.

An yi rawa tare da rera waƙoƙi a taron inda wasu daga cikinsu na suka gwamnatin jihar ne.

Wasu mata a wajen taron sun dinga ɗaga fallen zani ɗaya wanda ke nuni da cewar gwamnatin jihar “zango ɗaya” za ta yi.

A cikin waƙar, an dinga maimaita jimlar “Falle ɗaya ce In Sha Allahu”.

Magoya bayan sun riƙa rera waƙar tare da nuna goyon baya ta hanyar daga tutoci.

Fitar da wannan waƙa na nuna yadda ake amfani da kiɗa da al’adu a siyasar Kano wajen isar da saƙonni da kuma yin tasiri ga ra’ayin jama’a.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *