Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia

[ad_1]



’Yan sanda a kasar Indonesia sun ce an garzaya da daruruwan mutane zuwa asibiti bayan wani abu da ake zargin bam ne ya fashe a wani masallacin Juma’a da ke Jakarta babban birnin kasar.

Lamarin ya faru ne a lokacin sallar Juma’a a cikin wani ginin makaranta da ke Kelapa Gading, a arewaci Jakarta.

Kwamishinan ’yan sandan birnin, Asep Edi Suheri, ya ce har yanzu ana bincike don gano musabbabin fashewar.

Shaidun gani da ido sun ce sun ji fashewa biyu masu ƙarfi da misalin ƙarfe 12 na rana a agogon kasar, daidai lokacin da aka fara hudubar sallar Juma’a a masallacin.

Suheri ya ce an kai mutane 54, galibinsu ɗalibai zuwa asibiti da raunuka masu sauƙi da masu tsanani, ciki har da wadanda suka kone.

Ya ƙara da cewa mutum 20 na ci gaba da samun kulawa a asibiti, inda uku daga cikinsu ke fama da raunuka masu tsanani.

Suheri ya ce ƙungiyar ƙwararrun masu binciken bama-bamai da aka tura wurin ta gano bindigogin wasa da ƙaramar bindiga ta wasa a kusa da masallacin.

“’Yan sanda na ci gaba da binciken wurin don gano musabbabin fashewar,” in ji shi.

Kafafen yaɗa labarai na cikin gida a kasar sun nuna bidiyon da ke nuna layin ’yan sanda da ke kewaye da makarantar, inda motoci masu ɗaukar marasa lafiya ke tsaye a gefe.

Sai dai hotunan masallacin ba su nuna wata mummunar lalacewa ba sakamakon harin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *