Gwamnatin Tarayya ta haramta fitar da katako ƙasashen waje
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta kafa dokar haramta fitar da katako da kayayyakin da suka shafi itace daga Najeriya nan take, tare da soke dukkan lasisin yin haka da aka bayar a baya.
Ministan Muhalli, Balarabe Lawal, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin taron kwamitin kasa na muhalli karo na 18 da aka gudanar a Jihar Katsina.
Lawal ya ce wannan umarni, wanda aka tsara a cikin Dokar Shugaban Kasa mai taken “Dokar Shugaban Kasa kan Haramta Fitar da katako da Kayayyakin da suka shafi Itace, 2025,” ya zama dole domin dakile sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba da kuma lalata dazuka a fadin kasar.
Ya ce: “Dazukan Najeriya na da muhimmanci wajen dorewar muhalli, suna samar da iska da ruwa mai tsafta, suna tallafa wa rayuwar jama’a, suna kare nau’o’in halittu, tare da rage illolin sauyin yanayi.”
Ministan ya gargadi cewa ci gaba da fitar da itace yana barazana ga wadannan abubuwan da kuma lafiyar muhalli a nan gaba.
A karkashin wannan sabon tsari, hukumomin tsaro da ma’aikatun da abin ya shafa za su tabbatar da ɗaukar tsattsauran mataki a kan ayyukan sare itatuwa ba bisa ka’ida ba a fadin kasar.
A jawabinsa na buɗe taron, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Faruk Lawal Jobe, ya jaddada tarihin jihar wajen kafa manufofin zamantakewa da tattalin arziki da suka yi tasiri ga manufofin kasa.
Ya kuma yi nuni da muhimmancin hadin gwiwa wajen fuskantar kalubalen muhalli a fadin Najeriya.
Ya ce: “Dorewar muhalli na da matukar muhimmanci wajen cimma ci gaba da inganta rayuwar al’ummarmu. Gwamnatocinmu sun ba da fifiko ga shirye-shiryen yaki da kwararowar hamada da kuma inganta dasa itatuwa.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link