Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Ƙaramar Salla
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 19 ga watan Maris da Juma’a, 20 ga watan Maris, 2026 a matsayin ranakun hutu domin bikin ƙaramar salla, idan an kammala watan Ramadan.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya sanar da hakan a madadin gwamnati cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
- El-Rufai Ya Zargi ICPC Da DSS Kan Tsare Shi Ba Bisa Ƙa’ida Ba Da Neman Ya Yi Ritaya Daga Siyasa
- Harin Maiduguri: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Saƙon Trump A Kan Tinubu
Ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan, tare da ƙarfafa su da su ci gaba da yin riƙo da halaye na gari kamar soyayya, taimako, zaman lafiya, haƙuri da sadaukarwa.
Ministan ya kuma buƙaci dukkanin ’yan Nujeriya da su yi amfani da lokacin wajen yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
Ya ƙarfafi jama’a su yi bukukuwan cikin natsuwa tare da taimaka wa mabuƙata.
Ya ƙara da cewa gwamnati na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin ’yan Nijeriya.
[ad_2]
Source link