Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa za ta riƙa bai wa kowane masallacin Juma’a a jihar kuɗi daga Naira 300,000 zuwa 500,000 duk wata domin tallafa musu.

Haka kuma gwamnatin za ta riƙa biyan limaman masallatan, na’ibansu da ladanai alawus na kowane wata domin sauƙaƙa wa hidimominsu.

Mai magana da yawun gwamnatin, Abubakar Bawa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Ya ce manufar shirin shi ne ƙarfafa karatun Alƙur’ani da koyar da ilimin addini ga yara da matasa a jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu, ya sanar da wannan mataki ne a ranar Asabar yayin yaye ɗalibai 111 da suka kammala haddar Alƙur’ani a makarantar gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi da ke Sakkwato.

Ya ce alawus ɗin zai taimaka wajen ba malamai damar yin nazari da ci gaba da koyar da darusan addini.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta bayar da kwangilar gyara masallatai 65 na Juma’a, inda aka kammala 25, kuma aka riga aka buɗe 15 daga cikinsu.

Ya ce kula da harkokin addinin Musulunci na daga cikin manufofin gwamnatin sa, kuma ya ce yana da muhimmanci bayan batun tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *