Gwamnatin Kebbi ta ba da umarnin sake buɗe makarantu a jihar

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayar da umarnin buɗe dukkanin makarantun firamare da sakandare a faɗin jihar domin fara zangon karatu na biyu na shekarar 2025/2026.

Za a koma makarantun ne daga ranar Litinin, 5 ga watan Janairu, 2026.

An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Isah Ibrahim, jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Kebbi (SUBEB), da kuma Aliyu Bagarawa, Mataimakin Darakta (Ilimi) a Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Kebbi, suka sanya wa hannu.

Gwamnatin ta buƙaci shugabannin makarantu, malamai, iyaye, ɗalibai da jami’an ilimi da su bi umarnin da aka bayar.

An kuma umarci shugabannin makarantu da su yi dukkanin shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da dawowa makaranta cikin kwanciyar hankali.

An shawarci iyaye da su tabbatar ’ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci.

A wata sanarwa, an sanar da jami’an ilimi na yankuna, shugabannin sakandare, malamai masu kula da firamare da masu makarantu masu zaman kansu cewa mako na farko na dawowa makaranta za a sadaukar da shi ne domin gudanar da jarabawar zango na farko.

Za a fara karatu da darusa daga ranar Litinin, 12 ga watan Janairu, 2026.

Dukkanin makarantu dole ne su bi jadawalin dawowa da na jarabawa da gwamnatin jihar ta amince da su.

Tun da farko, gwamnatin jihar ta rufe makarantu bayan ’yan bindiga sun sace ’yan mata 25 daga Makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnati da ke Maga a watan Nuwamban 2025.

A yayin harin, mataimakin shugaban makarantar ya rasa ransa.

Gwamna Nasir Idris ya yi Allah-wadai da harin, tare da umartar sojoji da su gano wanda ya bayar da umarnin janye jami’an tsaro daga makarantar kafin aukuwar lamarin.

A ranar 25 ga watan Nuwamban 2025, gwamnan ya tabbatar da sakin ’yan matan da aka sace.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *